Connect with us

News

Magoya Bayan Kwankwasiyya Sun Zargi ‘Yan Daba Masu Alaka Da APC Da Tarwatsa Taron Su A Rogo

Published

on

Magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya a Jihar Kano sun zargi wasu ‘yan daba da suka ce na da alaka da jam’iyyar APC da kai hari tare da tarwatsa wani taron da suke gudanarwa a karamar hukumar Rogo.

Mai magana da yawun kungiyar, Habibu Sale Mohammed, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya aikawa manema labarai a ranar Lahadi.

Advertisement

Gwamnan Kano Ya Russhe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Wacce Mataimakinsa Yake Jagoranta A Matsayin Kwamishina

A cewarsa, lamarin ya faru ne yayin da magoya bayan tafiyar ke gudanar da wani taro cikin lumana domin karbar wasu sabbin mambobi da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP.

Advertisement

Sanarwar ta ce kafin gudanar da taron, sun sanar da jami’an ’yan sanda da kuma jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), don haka taron ya kasance bisa ka’ida.

Sai dai kungiyar ta yi zargin cewa wasu ‘yan daba dauke da makamai sun afka wajen taron, inda suka tarwatsa mahalarta tare da jikkata mutane da dama.

Advertisement

A cewar kungiyar, akalla mutane 11 sun jikkata sakamakon harin, ciki har da shugaban NNPP na karamar hukumar Rogo da kuma wani jigo da ya taba tsayawa takarar dan majalisar wakilai a karkashin PDP.

Magoya bayan Kwankwasiyya sun kuma yi zargin cewa an lalata akalla motoci uku, tare da wasu kayayyaki mallakin mambobinsu.

Advertisement

Kungiyar ta bayyana harin a matsayin wani yunkuri na dakile karuwar magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano, wadda ta ce tana ci gaba da samun sabbin mambobi daga wasu jam’iyyun siyasa.

Magoya bayan sun bukaci jami’an tsaro, musamman ’yan sanda da DSS, da su gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu a lamarin tare da daukar matakin doka a kansu.

Advertisement

Sai dai har zuwa yanzu, ba a samu martani daga jam’iyyar APC ko jami’an tsaro ba dangane da zargin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending