Connect with us

News

Hatsarin Jirgin Kasa Daga Abuja Zuwa Kaduna Ya Jikkata Mutane Da Dama

Published

on

1773704071560

Fasinjoji da dama sun jikkata bayan wani jirgin ƙasa da ke jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna ya sauka daga layin dogo sakamakon cin karo da wani abu a kan hanyarsa.

Lamarin ya faru ne yau Litinin a kusa da Asham a kan layin dogon da ke tsakanin Abuja da Kaduna, lamarin da ya jefa fasinjojin cikin fargaba.

Advertisement

Zabubbukan Shugabancin APC a Kano : Gwamna Abba Ya Cancanci Yabo Daga Hedikwatar Jam’iyya 

Shugaban Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa (NRC), Kayode Opeifa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an tura tawagar agajin gaggawa nan take bayan samun rahoton hatsarin.

Advertisement

Binciken farko ya nuna cewa jirgin ya kauce daga hanyarsa ne bayan ya yi karo da wani abu a kan layin dogon, sai dai har yanzu jami’ai ba su fitar da cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru ba.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin fasinjojin da suka samu raunuka daban-daban, an garzaya da su zuwa cibiyar lafiya da ke tashar jirgin ƙasa ta Idu da ke Abuja domin samun kulawar mahukuntan lafiya.

Advertisement

Hukumar NRC wadda ta tabbatar da faruwar hatsarin da misalin ƙarfe 10:30 na safiyar wannan Litinin, ta ce babu wanda ya rasa ransa a hatsarin.

Wasu hotuna da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna wasu daga cikin taragon jirgin da suka lalace, yayin da ma’aikatan jirgin ke duba inda abin ya faru, tare da ɗimbin fasinjojin da sun galabaita suka sauka daga jirgin suna jiran a kai su wuri mai aminci.

Advertisement

Hukumar NRC ta ce injin ɗaya daga cikin taragon jirgin da kuma wani tarago mai ɗaukar fasinja ne suka samu matsala sakamakon hatsarin

Opeifa ya ce an gaggauta aiwatar da matakan ceto tare da tura ƙwararrun jami’an fasaha zuwa wurin, yayin da Hukumar Tabbatar da Aminci (SIB) ke gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Advertisement

Ya kuma tabbatar da cewa jirgin ya isa tashar Idu da misalin ƙarfe 10:39 na safe, inda ya samu jinkiri na mintuna 38 saboda cire sassan jirgin da hatsarin ya shafa.

Hukumar ta jaddada cewa tsaron fasinjoji shi ne babban abin da ta sa a gaba, tare da tabbatar da cewa ana ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan jirgin cikin aminci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending