News
Kotu Ta Yanke Wa ‘Yan Fashi 4 Hukuncin Shekaru 10 a Gidan Yari A Kano
Babbar Kotun Jihar Kano karkashin jagorancin Mai Shari’a Adam Abdullahi a ranar Talata ta yanke wa wasu ‘yan fashi hudu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari tare da tara naira 10,000.
Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da: Shafi’u Abubakar, Usman Suleiman, Usman Sa’idu, da Ali Isa.
Gwamnatin Sokoto Ta Samu Yabo Kan Tallafa wa Marayu da Mabukata
An gurfanar da su bisa tuhuma uku, ciki har da hadin baki wajen aikata laifi da kuma fashi da makami, laifuka da ake hukunta su Karkashin Sashe na 97 da 298(c) na Kundin Laifuka.
Dukkan wadanda aka yanke wa hukuncin mazauna Rijiyar Lemo ne a Kano. Sun hada kai wajen aikata fashi da makami a wasu gidaje da ke unguwannin Sabon Garin Doka da Bankaura a karamar hukumar Ungogo.
Tuhuma ta Farko
A ranar 22 ga Yuli, 2024, tsakanin karfe 3:00 zuwa 4:00 na asuba, wadanda ake tuhuma sun shiga gidajen Abdullahi Musa (Unguwar Bankaura, Karamar Hukumar Ungogo) da Mansur Muazu (Sabon Garin Doka, Karamar Hukumar Ungogo) da makamai, suka kai musu hari, suka kwashe kayayyakin su. Wannan laifi yanyi karo da Sashe na 97 na Kundin dokar Laifuka.
Tuhuma ta Biyu
A wannan rana da karfe 3:00 na safe sun kai hari a gidan Abdullahi Musa a Unguwar Bankaura, Karamar Hukumar Ungogo, inda suka sace:
– Wayar Infinix mai darajar N50,000
– Wayar Tecno mai maballi darajar N5,000
– Babur Lifan mai darajar N700,000
– Kudi N800
Wannan laifi yana karkashin Sashe na 298(c) na Kundin Laifuka.
Tuhuma ta Uku
A karfe 4:00 na safe, 22 ga Yuli, 2024, sun kai hari a gidan Mansur Muazu a Sabon Garin Doka, Karamar Hukumar Ungogo, inda suka sace:
– Kudi N201,000
– Kudi 500 CFA
Wannan ma laifi ne karkashin Sashe na 298(c) na Kundin Laifuka.
Karanta Labari: Kotun Kano Ta Daure Matashi Shekaru 20 Tare Da Aikin Wahala Saboda Kashe Kawunsa
Lauyan gwamnati, Barrister Ibrahim Garba Arif, ya kira shaidu biyu don tabbatar da laifin.
A gefe guda, wadanda ake tuhuma karkashin jagorancin lauya Barrister Basira Yunus sun sauya jawabinsu daga “ba su aikata laifi ba” zuwa “sun aikata laifi.”
Kotun ta gudanar da shari’ar takaitacce, ta same su da laifi a dukkan tuhume-tuhume uku, saboda ikirarin aikata laifukan, sannan ta yanke musu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari tare da tara N10,000 kowanne.
Kotun ta bayar da umarni cewa hukuncin zai gudana a lokaci guda, tun daga ranar da aka kama su, wato 22 ga Yuli, 2024.
