News
Gwamnatin Zamfara Ta Haramta “Signing Out” Da Ɗalibai Ke Yi A Makarantu
Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Zamfara ta haramta bukukuwan “signing out” da ɗalibai ke yi a makarantu, tana mai cewa ayyukan sun fara wuce gona da iri, tare da nuna rashin ɗa’a da halaye da ba su dace ba.
Advertisements
Advertisements
A wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi, Abdulmalik Abubakar Gajam, ya sanya hannu, gwamnati ta umarci dakatar da duk irin waɗannan bukukuwa nan take tare da tabbatar da bin umarnin a makarantu.
Advertisements
Gwamnatin Zamfara Ta Haramta “Signing Out” Da Ɗalibai Ke Yi A Makarantu
Advertisements
Advertisements
An kuma gargaɗin malamai da ɗalibai cewa duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci mai tsauri, ciki har da dakatarwa ko soke sakamakon gama makaranta.
Advertisements
