News
An yi musayar bayanai tsakanin wakilan Amurka da Iran a Islamabad
An kammala zagaye na farko na tattaunawar tsagaita wuta ta kai tsaye tsakanin Amurka da Iran a Islamabad, babban birnin Pakistan.
Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif lokacin da yakee karbar baƙuncin tawagar Iran ƙarƙashin jagorancin shugaban Majalisar Dokokin ƙasar Mohammad Bagher Ghalibaf a birnin Islamabad.
Majiyoyi sun ce ɓangarorin biyu sun yi musayar bayanan da ke tabbatar da cewa suna kan fuska ɗaya kan yarjejeniyoyin da aka cimma a zagaye na farko na tattaunawar kai tsaye tsakanin gwamnatocin Washington da Tehran karon farko tun bayan juyin juya halin Musulunci na 1979.
Gwamnatin Tarayya Ta Tura Mutum 386 Gidan Yari Kan Laifukan Ta’addanci
Mataimakin shugaban Amurka JD Vance, wanda ke jagorantar tawagar Amurka, ya gana da Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif kafin tattaunawar kai tsaye, yayin da jami’an Iran, ciki har da Kakakin Majalisar Dokoki, Mohammad Bagher Ghalibaf da Ministan Harkokin Waje Abbas Araghchi, suma suka gana da Sharif.
Wannan tattaunawar na da nufin samar da yarjejeniyar zaman lafiya mai ɗorewa tsakanin Amurka da Iran bayan an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni biyu.
Har yanzu akwai rarrabuwar kawuna, musamman game da batun mashigin ruwa na Hormuz da kuma hare-haren da ke gudana a Lebanon, wanda Iran ta gindaya a matsayin sharadi kafin ci gaba da wasu matakan.
Sai dai kamfanin dillancin labarai na Pakistan wato Tasnim ya ruwaito cewa ɗaya daga cikin batutuwan da ke fuskantar rashin jituwa mai tsanani a tattaunawar shine batun mashigin Hormuz.
