News
Jami’an ’Yansanda Sun Kama Matasa Biyu Kan Zargin Hallaka Abokinsu A Wurin Casu
’Yan sanda a Jihar Adamawa sun kama wasu matasa biya bisa zargin kisan wani saurayi a yayin wani casu a Ƙaramar Hukumar Mubi ta jihar.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a wurin bikin zagayowar ranar haihuwa a unguwar Digil, inda ake zargin matasan sun soka wa mamacin mai suna Friday Isah wuƙa bayan wata taƙaddama ta ɓarke tsakaninsu.
An Gudanar da Bikin Aure Biyu a Sheka Achilafiya
Nguroje ya ce bayan jami’an tsaro na Mubi North sun samu rahoton, sai suka garzaya wurin tare da kai mamacin asibiti domin kulawa. Sai dai likita ya tabbatar da mutuwarsa daga baya.
A cewar sanarwar, wadanda ake zargi su ne Samson Elisha mai shekaru 19 daga Giye Digil da Ayuba Stephen mai shekaru 21 dukkansu an tsare su kuma bincike ya fara domin gano musabbabin kisan.
Kwamishinan ’Yan sanda na jihar, Kabir Umar Hassan, ya nuna takaici kan lamarin tare da umartar Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da su dauki nauyin shari’ar domin tabbatar da adalci.
Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ta ƙuduri aniyar ganin an hukunta masu laifi tare da kira ga al’umma su ci gaba da zama masu bin doka da oda, tare da sanar da duk wani abin da suka gani da ake zargin laifi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News7 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
