Connect with us

Politics

Ko Gawa Muka Tsayar Sai Ta Kayar Da Shugaba Tinubu A Zaɓen 2027 —Buba Galadima

Published

on

Buba Galadima

Jigo a jam’iyyar ADC, Buba Galadima, ya ce rashin jin daɗin da ‘yan Nijeriya ke ciki ya kai matakin da ko matacciyar gawa, idan ta shiga takara, za ta iya kayar da jam’iyyar APC a zaɓen 2027. Ya kuma zargi wasu da yunƙurin dakile taron jam’iyyar, yana mai jaddada cewa ba za su ja da baya ba duk da matsin lamba.

Galadima ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wani taron jam’iyyar a ranar Talata, inda ya soki salon mulkin jam’iyyar APC da kuma yadda take mu’amala da jam’iyyun adawa.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Ce Harin Dakarun Sojin Sama Na Jilli Ya Sauka Ne Kan Maɓoyar ‘Yan Ta’adda

A cewarsa, “Ko da babu wani mai rai a Najeriya, aka tsayar da gawa takara da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ina da tabbacin cewa gawa ce za ta yi nasara a zaɓen 2027.”

Advertisement

Ya kuma zargi APC da ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa da suka haɗa da PDP, SDP, NNPP, Labour Party da kuma ADC.

Galadima ya ce duk wani yunƙuri na tsoratarwa ko dakile ayyukan jam’iyyun adawa ya kamata su fuskance shi da jajircewa, yana mai cewa hakan ne kaɗai zai ba su damar kare dimokuraɗiyya.

Advertisement

Har ila yau, ya jaddada cewa ci gaba da gudanar da taron jam’iyyar duk da zargin matsin lamba daga masu mulki na nuna cewa ADC ba za ta bari a takaita mata ‘yancin gudanar da harkokin siyasa a ƙasar ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending