Connect with us

News

INNA LILLAHI WA INNA ILAYHI RAJI’UN: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Darikar Tijjaniyya  Sheikh  Warsu Kurna Rasuwa

Published

on

IMG 20260425 WA0027

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Allah ya yi wa babban malamin darikar Tijjaniyya a Jihar Kano, Sheikh Malam Warsu Kurna rasuwa.

Advertisement

Malamin ya rasu ne da safiyar ranar Asabar, 25 ga watan Afrilun shekarar 2026, kamar yadda Ɗansa Umar Warsu ya tabbatar.

Abin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini

Advertisement

Tuni aka gudanar da jana’izarsa a makabartar Kurna, inda dimbin al’umma, ciki har da malamai, dalibai da mabiyansa suka halarta domin yi masa addu’ar karshe.

Marigayin ya shahara wajen koyar da ilimin addinin Musulunci da kuma tarbiyyantar da al’umma, inda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yada ilimi da kuma jagorantar jama’a kan harkokin addini a yankin Kurna da ma sauran sassa na jihar Kano.

Advertisement

Rasuwarsa ta jawo alhini a tsakanin al’umma da dama, inda mutane ke bayyana shi a matsayin babban rashi ga harkokin addini da rayuwar al’umma, tare da cewa za a jima kafin a samu wanda zai cike giɓin da ya bari.

Allah Ya jikansa da rahama, ya kuma ba iyalansa da al’ummar Musulmi hakurin jure wannan rashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending