News
Wata Tankar Mai Ta Fashe A kaduna
Mutane biyu sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a hanyar Bypass da ke Kaduna, kusa da yankin Sabuwar Fanteka.
Ammasco Radio ta ruwaito cewa wata motar tanker mai ɗauke da mai ce ta take mutanen, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsu nan take a wurin.
Hatsarin ya janyo tashin hankali a yankin, inda wasu matasa suka nuna ɓacin rai tare da yunƙurin banka wa motar wuta sakamakon fushin da suka nuna kan faruwar lamarin.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da hatsarin ko matakan da aka ɗauka domin daƙile tarzomar da ta biyo baya.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
