News
Siyasa Ce Ta Fi Dacewa Da Malamai Ba Kamasho Ba —Malam Ibrahim Khalil
Sheikh Ibrahim Khalil, fittacen malamin addinin Musulunci kuma shugaban majalisar malamai a Kano, ya bayyana cewa ya fi dacewa malamai su shiga harkokin siyasa maimakon ci gaba da zama cikin abin da ya kira “kamasho” a halin yanzu.
Malamin ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Matashiya TV, inda ya jaddada cewa tun tarihi malamai su ne suka kasance a matsayin shugabannin al’umma.
Jami’an ‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Fashi Da Makami A Kaduna
A cewarsa, kasancewar malamai suna da ilimi da fahimtar al’amuran rayuwa, ya kamata su taka rawar gani a siyasa domin ba da gudunmawa wajen inganta shugabanci.
“Bai dace malamai su zama ‘yan kamasho kamar yadda ake gani a yanzu ba. Siyasa ita ce hanya mafi dacewa da za su bi domin kawo gyara a al’umma,” in ji shi.
Ya kuma kara da cewa shigar malamai cikin siyasa na iya taimakawa wajen samar da shugabanci nagari da kuma ci gaban kasa.
