News
Kotun Koli Da Gwamna Abba Ne Kadai Ke Da Wuka Da Nama Kan Batun Masarautar Kano —Ganduje
Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa Kotun Kolin Nijeriya ce kadai ke da ikon yanke hukunci kan rikicin sarautar Kano.
Ganduje ya ce duk hukuncin da kotun koli ta yanke, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai mutunta shi tare da aiwatar da shi bisa doka da oda.
Gwamnatin Tarrayya Ta Haramta Sanya ‘Dr’ Ga Sunayen Wadanda Aka Ba Digirin Girmamawa
Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa ya amince da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Kano.
Sai dai Ganduje ya ce rahotannin ba gaskiya ba ne, yana mai jaddada cewa kotu ce za ta yanke hukunci na karshe kan rikicin sarautar.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
