News
Ciyawa Mai Guba Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Shanu 80 A Adamawa
Wani abu da ake zargi gubar ciyawa ce, ta yi sanadiyyar mutuwar shanu sama da 80 a kauyen Chafajaule a gundumar Ribadu da ke Karamar Hukumar Fufore ta Jihar Adamawa.
Duba da irin dimbin asarar da masu shanun da annobar ta shafa suka tabka, biyo bayan cin ciyawar wacce ake yi wa lakabi da Fulfulde ko kuma ngayari, iftila’in na ci gaba da jefa matukar fargaba, a zukatan sauran masu kiwon shanu a yankin.
Ciyawa Mai Guba Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Shanu 80 A Adamawa
Daraktan kula da lafiyar dabbobi na Adamawa, Dakta Bartholomew Nyalas, yayin da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin ya ce, mai yiwuwa shanun sun mutu ne, bayan cin wata tsohowar ciyawa wacce ruwan sama na farko, ya sauka a kanta.
Nyalas ya kara da cewa, a kan samu afkuwar irin wannan lamarin, wanda kuma ya ke haddasa mutuwar shanu nan take da suka ci irin wannan ciyawa mai dauke da guba.
Kazalika, ya bukaci al’ummar jihar da su gaggauta kai rahoton bullar duk wata cuta da suke zargin na kama dabbobi a ofis-ofis na duba lafiyarsu da ke kananan hukumomin jihar 21, domin a dauki matakan gaggawa.
Shi kuwa, kwamishinan kula da bunkasa kiwon dabbobi da aikin noma na jihar, Sa’idu Idris, a nasa bangaren ya ce; tuni gwamnatin jihar ta dauki matakan gaggawa ta hanyar gano shanun da suka kamu da cutar da kuma lalata su, domin gujewa yaduwar cutar zuwa sauran garken da ake kiwata sauran shanu a jihar.
Kazalika Idris ya kara da cewa, tuni ma’aikatarsa ta bayar da umarnin a tura nau’in cutar zuwa cibiyar binciken lafiyar dabbobi ta BOM da ke garin Jos na Jihar Filato, domin zurafa gudanar da bincike kan cutar.
Haka zalika, ya yaba wa ma’aikatan karamar hukumar ta Fufore, a kan saurin sanar da bullar cutar wanda hakan ya taimaka wajen kare daruruwan shanun da ke yankin daga kamuwa da cutar.
