Connect with us

News

Rikici Kan Rabon N8,000 Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi

Published

on

police arrest

Wani rikici da ya ɓarke kan rabon kuɗin da aka tara yayin bikin gargajiyar Egungun a garin Ilare da ke Jihar Osun, ya yi ajalin wani matashi mai suna Bukunmi.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Juma’a bayan wasu matasa uku — Bukunmi, Femi da Pelumi — sun gudanar da jerin gwanon bikin Egungun tare da karɓar kuɗi daga jama’a.

Advertisement

Rami Ya Rufta Da Mutum 5 Masu Haƙar Zinari Ba Bisa Ƙa’ida Ba  ‎

Majiyoyi daga yankin sun ce rikicin ya samo asali ne lokacin da matasan suka fara rabon kuɗi kimanin N8,000 da suka tara yayin bukin.

Advertisement

Wata majiya ta shaida cewa, da misalin ƙarfe 7:30 na yamma, matasan suna ci gaba da shagulgulan bikin kafin daga bisani suka zauna domin raba kuɗin da suka samu.

A cewar majiyar, rikici ya kaure tsakanin Pelumi da Bukunmi, waɗanda aka ce ‘yan gida ɗaya ne, lamarin da ya sa Femi ya shiga tsakani domin sasanta su tare da hana faɗa.

Advertisement

Sai dai ana zargin Bukunmi ya kai wa Femi hari tare da bugunsa a baki, abin da ya haddasa ɓacin rai, inda ake zargin Femi ya caka masa wuƙa.

Nan take aka garzaya da Bukunmi zuwa asibiti domin ceto rayuwarsa, sai dai daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa sakamakon raunukan da ya samu.

Advertisement

Rahotanni sun ce wasu fusatattun matasa sun yi yunƙurin kai hari ga Femi bayan faruwar lamarin, amma jami’an Hukumar Tsaro ta NSCDC sun isa wurin cikin gaggawa tare da ceto shi kafin daga bisani suka miƙa shi ga ‘yan sanda a sashen Esa Oke.

An kuma ce ‘yan sanda sun kwashe gawar mamacin tare da wuƙar da ake zargin an yi amfani da ita wajen aikata laifin domin gudanar da bincike.

Advertisement

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Osun, Abiodun Ojelabi, ya ce ana tsare da wanda ake zargi yayin da bincike ke gudana.

Ya ce, “Mun samu rahoton faruwar lamarin. Wanda ake zargi yana hannun ‘yan sanda, yayin da aka ajiye gawar mamacin a ɗakin ajiyar gawa domin gudanar da binciken likita. Bincike yana ci gaba domin gano musabbabin aukuwar lamarin.

Advertisement

 

 

Advertisement

PLATINUM POST NEWS 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending