News
Iran Ta Rataye Mutumin Da Ya Yi Wa Amurka Da Isra’ila Leƙen Asiri
Iran ta sanar a ranar Litinin cewa ta rataye wani mutum da aka samu da laifin yi wa Isra’ila da Amurka leƙen asiri, a wani mataki na ƙara ƙaimi kan hukuncin kisa da ƙasar ke aiwatarwa tun bayan ɓarkewar yaƙinta da ƙasashen biyu.
Shafin Mizan Online a Iran ya bayyana cewa an rataye Erfan Shakourzadeh ne bayan samunsa da laifin haɗa kai da hukumar leƙen asirin Amurka ta CIA da kuma Mossad ta Isra’ila.
Tirela Ta Kife A Gadar Lado Da Ke Kano
Sai dai mahukuntan Iran ba su bayyana lokacin da aka kama shi ko ranar da aka aiwatar da hukuncin kisan ba.
Rahoton ya ce mutumin yana aiki ne a ɗaya daga cikin cibiyoyin kimiyya na Iran masu alaƙa da harkokin tauraron ɗan adam.
Ƙasashen yamma sun daɗe suna zargin Iran da amfani da shirinta na tauraron ɗan adam wajen bunƙasa fasahar makamai masu linzami masu cin dogon zango, zargin da Tehran ke musantawa.
A cewar Mizan Online, Shakourzadeh “bisa ra’ayinsa na ƙashin kai” ya riƙa bai wa CIA da Mossad wasu bayanan sirri.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun bayyana Iran a matsayin ƙasa ta biyu mafi yawan aiwatar da hukuncin kisa a duniya bayan China.
Ƙungiyar Iran Human Rights mai hedikwata a Norway ta ce Iran ta kashe mutum fiye da 1,500 a shekarar da ta gabata, adadin da ke zama mafi girma a duniya.
Tun bayan fara yaƙi tsakanin Iran da Isra’ila da Amurka a ƙarshen watan Fabrairu, Iran ta ƙara ƙaimi wajen aiwatar da hukuncin kisa, musamman a shari’o’in da suka shafi zargin leƙen asiri da barazanar tsaro.
A makon da ya gabata ma, Tehran ta rataye wasu mutum uku da aka samu da hannu a zanga-zangar adawa da gwamnati da ta girgiza ƙasar a watan Disamba da Janairu.
