News
Kano: Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Gwarzo
Al’ummar garin Lakwaya da ke Ƙaramar Hukumar Gwarzo a Jihar Kano sun sake shiga cikin fargaba bayan wasu ’yan bindiga da ake zargin ɓarayin shanu ne sun kai sabon hari a yankin, kwana ɗaya bayan wani makamancin farmaki.
Dagacin Lakwaya, Alhaji Idris Adamu Danbarugu, ya bayyana cewa maharan sun afka wa garin ne da yammacin ranar Alhamis, daf da lokacin Sallar Magariba, inda suka shiga ta ƙofar fada tare da kora shanu zuwa yankin Rugoji.
Tukin Ganganci Yayin Kai Amarya Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi
Ya shaida cewa maharan sun yi harbe-harbe domin firgita mazauna yankin kafin su tsere da dabbobin.
A cewarsa, har zuwa lokacin da yake magana da manema labarai, jami’an tsaro ba su kai ɗauki yankin ba duk da kiran gaggawar da aka yi musu.
Rahotanni sun kuma nuna cewa mutum biyu sun samu raunukan harbin bindiga yayin harin, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin jimami da tashin hankali.
Premier Radio ta rawaito cewa mazauna yankin sun buƙaci hukumomin tsaro da gwamnatin jihar su ƙara kaimi wajen samar da tsaro domin dakile hare-haren da suka fara addabar yankin Gwarzo da kewaye.
