Connect with us

News

Zanga-Zangar Rashin Tsaro A Kano: Matashi Ya Mutu, An Kona Ofishin Ƙaramar Hukuma A Gwarzo

Published

on

IMG 20260517 WA0052 (1)

Wani matashi ya rasa ransa yayin wata zanga-zangar adawa da yawaitar hare-haren ’yan bindiga da matasa suka gudanar a Ƙaramar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano.

Zanga-zangar, wadda ta gudana a ranar Lahadi, ta biyo bayan ƙara yawaitar hare-haren satar shanu, garkuwa da mutane da kashe-kashe da ake zargin wasu ’yan bindiga daga yankunan Jihar Katsina na kai wa al’ummomin yankin.

Advertisement

Rikicin CSO A Kano: Lokaci Ya Yi Na Haɗin  Gwiwa Domin Kare Manufofin “Kano First” ‎

Rahotanni sun ce fusatattun matasan sun kuma banka wa wani sashe na sakatariyar Ƙaramar Hukumar Gwarzo wuta tare da ƙona tayoyi a manyan hanyoyi domin nuna fushinsu kan matsalar rashin tsaro.

Advertisement

Masu zanga-zangar sun toshe hanyar Kano zuwa Gwarzo da Dayi na sa’o’i da dama, abin da ya haddasa cunkoso da tsaikon zirga-zirga ga matafiya da direbobi masu amfani da hanyar.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ana zargin hayaƙin barkonon tsohuwa da kuma tayoyin da aka ƙona ne suka yi sanadiyyar mutuwar matashin a yayin rikicin.

Advertisement

Majiyoyi sun ce matasan sun fara taruwa ne daga Kwanar Lakwaya kafin daga bisani su kutsa cikin garin Gwarzo, inda suka ci gaba da zanga-zangar tare da kai hari sakatariyar ƙaramar hukumar.

Mazauna yankin sun nuna damuwa kan yadda hare-haren ’yan bindiga suka ƙara tsananta a yankin cikin kwanakin baya, lamarin da suka ce ya jefa jama’a cikin tsoro da rashin kwanciyar hankali.

Advertisement

Sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace domin kawo ƙarshen hare-haren da kuma kare rayuka da Dunkin al’umma.

 

Advertisement

 

Aminiya

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending