Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Gano Tarin Harsasai Da Aka Ɓoye A Cikin Garin Kwaki A Kaduna 

Published

on

IMG 20260518 013903 001

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, sun yi nasarar kama harsasai guda guda 1,989 da aka ɓoye cikin buhunan garin kwaki a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce jami’an hukumar sun samu nasarar cafke wani mutum mai suna Abdullahi Hassan mai shekara 35 ɗauke da harsasan ƙirar RLA 7.62mm da aka ɓoye cikin farin garin kwaki domin kauce wa binciken jami’an tsaro.

Advertisement

Matatar man Dangote Ta Maka Hukumar NMDPRA A Gaban Kotu

Sanarwar ta ce an kama wanda ake zargin ne yayin sintirin jami’an NDLEA a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ranar 12 ga watan Mayun 2026, kafin daga bisani a miƙa shi tare da kayayyakin da aka kama ga wata hukumar tsaro domin zurfafa bincike.

Advertisement

Hakazalika, hukumar ta ce jami’anta sun kai samame a yankin Dan Magaji da ke Zariya a Jihar Kaduna, inda suka ƙwato kilo 361 na tabar wiwi tare da cafke wani mutum mai suna Husaini Suleiman mai shekara 42.

 

Advertisement

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending