News
Peter Obi Ya Zaɓi Kwankwaso A Matsayin Abokin Takararsa
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya zaɓi tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin abokin takararsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Obi ya sanar da hakan ne a ranar Asabar yayin jawabinsa na karɓar takara bayan da aka tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a wani taro na musamman da aka gudanar a Abuja.
Shari’o’in Zaɓe: Kotu Ta Kawo Sabon Tsari Don Kauce Wa Ƙarewar Wa’adi
Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya zama ɗan takara shi kaɗai a zaɓen fidda-gwani na jam’iyyar da aka gudanar a ranar 29 ga watan Mayu, 2026.
An amince da takararsa ne bayan wani ƙuduri da Sanata Victor Umeh ya gabatar, yayin da tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege, ya mara masa baya.
Bayan tabbatar da takarar, jagoran jam’iyyar NDC, Sanata Seriake Dickson, da Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Cleopas Moses Zuwoghe, sun miƙa masa tutar jam’iyyar.
