Connect with us

News

An Rufe Shagunan Sayar Da Magani Kusan 600 A Plateau

Published

on

thuoc thiet yeu.tmb 1024v

Cibiyar kula da samar da maguguna a Najeriya ta ƙulle wasu shagunan sayar da magunguna har 572 a jihar Plateu kaɗai, waɗanda ta ce suna gudanar da ayyukansu ba bisa ƙa’ida ba.

Bayanai sun ce an ƙulle shagunan ne sakamkon dalilai mabanbanta da suka ci karo da dokokin cibiyar, ciki kuwa har da sayar da ƙwayoyin sanya maye, ko kuma magungunan da suka masu sha ke amfani da su don yin maye.

Advertisement

ADC Na Neman Raba Gawuna Da Tsarin NDC Kwankwasiyya Bayan Yimasa Tayin Takarar Gwamnan Kano A 2027

Shugaban sashen kula da dokoki na cibiyar Dr Sulaiman Chiroma ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Jos, bayan kammala ran gadin da aka gudanar na tsahon kwanaki 4.

Advertisement

Chiroma wanda ya yi jawabi a madadin shugaban cibiyar Ibrahim Ahmed ya ce an gudanar da wannan aiki ne ƙarƙashin sashe na 31 na kundin dokokin da suka kafa cibiyar na shekarar 2022.

A cewar sa wannan na cikin yunƙurin da cibiyar ke yi na taimakwa hukumomin Najeriya wajen kawo ƙarshen shan magungunan asibiti don yin maye da kuma kakkaɓe sayarwa da jama’a jabun magunguna.

Advertisement

A Najeriya dai ana samun ƙaruwar masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, musamman ta hanyar amfani da magungunan asibiti da ake samu a irin waɗannan ɗakunan shan magunguna.

 

Advertisement

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending