News
Mutane 3 Sun Mutu Yayin Da Jirgin Ƙasa Ya Kife A Hanyar Warri Zuwa Itakpe
An tabbatar da mutuwar fasinjoji uku bayan wani jirgin ƙasa da ke tafiya tsakanin Warri da Itakpe ya kife a ranar Litinin, lamarin da ya tayar da hankalin jama’a a Najeriya.
Hukumar Kula da Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta tabbatar da aukuwar hatsarin, inda ta ce an tura jami’an agajin gaggawa da sauran hukumomin da abin ya shafa domin kai ɗauki da kuma gudanar da aikin ceto.
An Gano Matar Da Aka Ce An Yi Garkuwa Da Ita Tare Da Masoyinta A Otal Bayan Neman Kuɗin Fansa
A cikin wata sanarwa da Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Hukumar, Kayode Opeifa, ya fitar, NRC ta ce tana ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki tare da tattara bayanai kan musabbabin hatsarin.
Sanarwar ta ce: “Mun tabbatar da aukuwar wani hatsari da ya shafi jirgin Warri–Itakpe Train Service (WITS) a yau. Jami’an ceto da hukumomin da abin ya shafa suna wurin domin taimaka wa fasinjoji da kuma kula da lamarin.”
Hukumar ta ƙara da cewa za ta fitar da cikakken bayani ne da zarar an kammala bincike da tantance ainihin abin da ya faru.
A nasa ɓangaren, Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da mutuwar fasinjoji uku, inda ta ce an kammala tantance dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin tare da fara aikin ceto nan take.
Fadar ta kuma yi kira ga jama’a da su guji yaɗa jita-jita, su riƙa dogaro da sahihan bayanai daga hukumomin da abin ya shafa.
Wannan lamari ya faru ne ƙasa da wata guda bayan dakatar da zirga-zirgar jirgin Warri–Itakpe na wani lokaci, domin yin gyare-gyare da ƙarin binciken tsaro daga injiniyoyi.
A yanzu haka ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin kifewar jirgin tare da matakan da za su hana faruwar irin wannan lamarin a nan gaba.
