Connect with us

News

An Cafke Matar Da Ta Yi Karyar Cewa ‘Yan Bindiga Sun Sace Ta A Dakin Otel Da Masoyinta

Published

on

Married 768x559

Jami’an tsaro sun kama wata matar aure mai suna Oluchi bayan zargin cewa ta shirya garkuwa da kanta domin karɓar kuɗin fansa daga hannun ’yan uwanta da abokan arziki.

Rahotanni sun nuna cewa an gano matar tare da wani mutum da ake zargin saurayinta ne a wani otel da ke yankin Ubiaroko na Jihar Delta, bayan binciken da jami’an tsaro suka gudanar.

Advertisement

SCSN Ta Nuna Fushinta Kan Taɓarɓarewar Tsaro, Ta Buƙaci Gwamnati Ta Ɗauki Mataki Cikin Gaggawa

Lamarin ya fara ne lokacin da iyalan matar suka kai rahoton cewa an yi garkuwa da ita a yankin Ikpoba Hill da ke Ƙaramar Hukumar Ikpoba-Okha a Jihar Edo. Bayan haka, an fara neman kuɗin fansa har Naira miliyan 50, wanda daga baya aka rage zuwa Naira miliyan 20.

Advertisement

A sakamakon haka, ’yan uwa da abokan arziki sun fara tattara gudunmawar kuɗi domin ceton ta, yayin da ’ya’yanta suka nemi taimakon jama’a.

Sai dai binciken da jami’an tsaro suka gudanar ya gano cewa matar ba ta hannun masu garkuwa ba ce. Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa jami’an tsaro sun bi sawun wata lambar waya da ake zargin tana da alaƙa da lamarin, lamarin da ya kai su wani otel a Jihar Delta.

Advertisement

“Bayan bin sawun lambar wayar, jami’an tsaro sun gano mutumin da ake zargi, kuma lokacin da suka isa otel ɗin, sun tarar da shi tare da matar da aka ce an yi garkuwa da ita,” in ji majiyar.

Bayan gano hakan, an sanar da mijin matar da sauran ’yan uwanta halin da ake ciki.

Advertisement

A wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta, Anita, ɗiyar matar da ke zaune a ƙasar Canada, ta bayyana kaɗuwarta da sakamakon binciken.

Ta ce iyalansu sun yi duk mai yiwuwa domin ceton mahaifiyarta, tare da haɗa kai da jami’an tsaro wajen gudanar da bincike.

Advertisement

“An sanar da mu cewa an gano mahaifiyata lafiya, amma daga baya aka gaya mana cewa tana da hannu a lamarin. Mun yi duk abin da muka yi ne domin kare rayuwarta,” in ji Anita.

Ta ƙara da cewa iyalansu ba su biya ko kwabo ɗaya a matsayin kuɗin fansa ba, kuma duk kuɗaɗen da aka tara domin ceton matar za a mayar wa masu su.

Advertisement

Anita ta kuma ce masu bincike sun shaida musu cewa an yi zargin mahaifiyarta da mutumin da aka kama tare da ita sun shirya yadda za su amfana da wani kaso daga cikin kuɗaɗen fansar da aka tara.

Lamarin ya jefa iyalan matar cikin ruɗani da takaici, musamman ganin cewa mahaifinsu na fama da rashin lafiya a lokacin da aka fara yaɗa labarin sacewar.

Advertisement

Haka kuma, ƙungiyar Harmony Ladies Club, wadda Anita ke cikinta, ta bayyana rashin jin daɗinta kan yadda lamarin ya kasance bayan ta bayar da gudunmawar kuɗi da sauran tallafi domin taimakawa wajen neman ceton matar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, CSP Moses Yamu, ya ce an kama mutum huɗu da ake zargi da hannu a wannan al’amari.

Advertisement

“Zan iya tabbatar da faruwar lamarin, kuma an kama mutum huɗu da ake zargin suna da hannu a ciki. Bincike na ci gaba da gudana domin gano cikakken yadda aka shirya lamarin,” in ji Yamu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending