News
Oshiomhole Ya Nemi a Kama Tsohon Shugaban NNPCL, Mele Kyari
Sanata Adams Oshiomhole ya yi kira da a gaggauta kama tsohon Babban Daraktan NNPCL, Mele Kyari, kan zarge-zargen cin hanci da rashin gudanar da kuɗaɗen gwamnati yadda ya kamata.
Oshiomhole ya zargi Kyari da kasa yin bayanin yadda aka tafiyar da tiriliyoyin nairori a lokacin da yake jagorantar NNPCL.
Mamakon Ruwan Sama Da Iska Mai Ƙarfi Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Kaka Da Jikarta A Bauchi
Ya kuma ce bai kamata kwamitin da ke binciken lamarin ya yi jinkiri wajen amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi ba domin tabbatar da gaskiya da ɗaukar matakin da ya dace ba.
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan yadda aka gudanar da harkokin kamfanin mai na ƙasa a shekarun baya.
Advertisements
