News
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi Allah-wadai da wani hukuncin da ake zargin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke na neman cireta daga rijista, inda ta bayyana matakin a matsayin barazana ga dimokuradiyyar Nijeriya tare da gargadin cewa bai kamata a yi amfani da bangaren shari’a wajen raunana jam’iyyun adawa ba.
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar na Ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Litinin, jam’iyyar ta zargi wasu jami’an gwamnati da goyon bayan yunkurin kawar da ita da sauran jam’iyyun adawa daga fagen siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027.
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Bisa Zargin Saran Mijinta Da Adda
ADC ta nuna damuwa kan wani hukunci da ake cewa Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke a karar da wata ƙungiya mai suna National Forum of Former Legislators ta shigar, tana neman a soke rijistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu.
Jam’iyyar ta ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta riga ta shaida wa kotu cewa ADC ba ta karya wata doka ko sharadin da zai sa a cireta daga rijista ba.
Haka kuma, ta yi zargin cewa kotun ta ci gaba da sauraron shari’ar duk da kasancewar umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya dakatar da shari’ar yana nan daram.
ADC ta yi ikirarin cewa karar wani ɓangare ne na yunƙurin da ake yi na raunana jam’iyyun adawa kafin zaɓen 2027.
Ta kuma yi gargadin cewa duk wani ƙoƙari na hana babbar jam’iyyar adawa shiga zaɓe na iya haifar da matsala ga zaman lafiyar siyasa da kuma tauye damar zaɓin da al’umma ke da ita.
Jam’iyyar ta bayyana cewa za ta kalubalanci hukuncin ta hanyar amfani da duk hanyoyin shari’a da kundin tsarin mulki ya tanada.
Haka kuma, ta ce za ta kai ƙorafi ga Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta Ƙasa (NJC) kan abin da ta kira rashin bin ƙa’idojin aikin shari’a da mai shari’ar ya nuna.
Da take sake jaddada aniyarta ta shiga zaɓen gama-gari na 2027, ADC ta bukaci mambobinta da magoya bayanta da su kasance cikin natsuwa, tana mai cewa za ta kasance cikin jam’iyyun da za su fafata a zaɓen matuƙar za a gudanar da shi.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, bangaren shari’a da sauran waɗanda aka ambata a cikin sanarwar ba su fitar da wata amsa kan zarge-zargen da jam’iyyar ta yi ba.
