News
Wasu Fisatattun Matasa Sun Ƙone Wata Mata Ƙurmus Kan Jita-Jitar Satar Yara A Kaduna
Wata mata mai suna Malama Ummulkhairi ta rasa ranta bayan da wasu fusatattun matasa suka yi mata dukan tsiya tare da ƙona gawarta a yankin Marabar Jos da ke Jihar Kaduna, sakamakon zargin satar yara da har yanzu ba a tabbatar da gaskiyarsa ba.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da tayar da hankali, tana mai yin Allah-wadai da abin da ta kira ɗaukar doka a hannu.
JAMB Ta Soke Karatun Digirin Hadin Gwiwa Da Kwalejojin Ilimi A Najeriya
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce jami’an tsaro sun samu nasarar ceto matar daga hannun wasu mutane da suka far mata da safiyar ranar da lamarin ya faru.
A cewarsa, an kai matar ofishin ’yan sanda domin ba ta kariya tare da fara bincike kan zargin da ake yi mata. Sai dai daga baya, ɗaruruwan mutane sun mamaye ofishin ’yan sandan tare da ƙwace matar daga hannun jami’an tsaro.
Shaidu sun ce mutanen sun yi mata mummunan duka har ta mutu, kafin daga bisani su banka wa gawarta wuta.
Lamarin ya jawo martani daga ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama, ciki har da Amnesty International, waɗanda suka yi kira ga hukumomi da su gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin da kuma hukunta masu hannu a ciki.
An bayyana marigayiyar a matsayin mahaifiya ga yara biyar, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin jama’a da ƙungiyoyin farar hula.
Rundunar ’yan sandan ta ce tuni ta kama wasu daga cikin waɗanda ake zargi da hannu a wannan aika-aika, yayin da ake ci gaba da neman sauran da suka tsere.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna ya yi gargaɗi ga jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, yana mai jaddada cewa duk wanda aka samu da hannu a lamarin zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
