News
KPCF Ta Yaba Wa Waiya Kan Inganta Hulɗar Gwamnati Da Jama’a A Kano
Gamayyar Kungiyoyin Fararen Hula Masu Kishin Jihar Kano (KPCF), wadda ta ƙunshi sama da kungiyoyi 451, ta yabawa Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, bisa abin da ta bayyana a matsayin jagoranci nagari da kuma ƙoƙarinsa na ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnatin jihar da kungiyoyin fararen hula.
A cikin wata sanarwa da gamayyar ta fitar ranar Laraba, ta ce matakin da ma’aikatar ta ɗauka na farfaɗo da Sashen Ayyuka na Musamman (Special Assignments Department) ya samar da wata ingantacciyar hanya ta tattaunawa, tuntuba da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kungiyoyin fararen hula a jihar.
Amurka Ta Kakaba Takunkumi A Kan Wani Dan Canji Dan Najeriya Da Kamfanoni Uku A Kano Da Largos
Kungiyar ta bayyana cewa matakin ya ƙara bai wa al’umma damar shiga cikin harkokin mulki da bayar da gudunmawa wajen tafiyar da al’amuran jama’a.
KPCF ta kuma yaba wa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa rungumar tsarin shugabanci mai haɗa kowa da kowa, tare da amincewa da muhimmiyar rawar da kungiyoyin fararen hula ke takawa wajen bunƙasa ci gaban al’umma.
Sanarwar ta ce ƙarƙashin jagorancin Kwamared Waiya, Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida ta ƙaddamar da jerin tarurruka da zaman tattaunawa da kungiyoyin fararen hula a faɗin jihar, lamarin da ya samar da damar musayar ra’ayoyi kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati, tare da ƙarfafa haɗin kai wajen magance matsalolin da suka shafi jama’a.
Ta ƙara da cewa wannan tsari ya zama wata muhimmiyar hanya ta isar da koke-koke, damuwa da shawarwarin al’umma zuwa ga gwamnatin jihar domin ɗaukar matakan da suka dace.
A cewar kungiyar, tsawon lokaci an samu gibi a fannin sadarwa da amincewa tsakanin hukumomin gwamnati da kungiyoyin fararen hula, amma sabbin matakan da Kwamishina Waiya ya jagoranta sun taimaka wajen cike wannan gibi tare da samar da sabon yanayi na fahimtar juna, mutunta juna da haɗin gwiwa.
Kungiyar ta ce hakan ya ƙara inganta gaskiya, riƙon amana da kuma shugabanci da ke bai wa muradun jama’a fifiko a Jihar Kano.
Haka kuma, KPCF ta yabawa Kwamared Waiya bisa rawar da yake takawa wajen aiwatar da shirin Safe Corridor Kano Model, wanda ke mayar da hankalinsa kan gyarawa, ƙarfafawa da sake haɗa matasan da suka tuba da al’umma.
A cewar kungiyar, shirin ya nuna aniyar gwamnati wajen magance matsalolin daba, rikice-rikicen siyasa, aikata laifuka, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran munanan dabi’u ta hanyar lumana da dabarun da za su samar da mafita mai ɗorewa.
Kungiyar ta sake jaddada goyon bayanta ga Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, tare da kira ga gwamnatin jihar da ta ci gaba da ƙarfafa irin waɗannan hanyoyin hulɗa domin tabbatar da cewa ra’ayoyin jama’a suna ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofi da shirye-shiryen ci gaban jihar.
Ta kuma buƙaci dukkan kungiyoyin fararen hula a Kano da su yi amfani da wannan dama wajen gina haɗin gwiwa mai amfani da gwamnati domin inganta zaman lafiya, ci gaba, haɗin kai da shugabanci nagari.
Sanarwar ta samu sa hannun Jagoran Gamayyar Kungiyoyin, Mustapha Muhammed Chiroma, tare da mataimakansa Ibrahim Hassan Gama da Peter Hassan Tijjani.
