News
Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki A Jami’o’in Jihohi 11

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yi barazanar ƙaddamar da yajin aiki na sai baba-ta-gani a jami’o’in jihohi 11, idan gwamnatocin jihohin da abin ya shafa ba su cika alƙawuran da suka ɗauka a yarjejeniyar da aka cimma da ƙungiyar a shekarar 2025 ba kafin ƙarshen watan Yuli.
Shugabannin shiyyoyin Benin da Yola na ASUU ne suka bayyana hakan a tarukan manema labarai daban-daban da suka gudanar a ranar Litinin, inda suka nuna damuwa kan yadda wasu gwamnatocin jihohi suka gaza aiwatar da muhimman tanade-tanaden yarjejeniyar.
KANO: Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Jikkata Mutum 12 A Warawa
Jihohin da ASUU ta ce matsalar ta shafa sun haɗa da Edo, Delta, Ondo, Adamawa, Borno, Taraba da Yobe, tare da wasu jami’o’in jihohi da suka kai adadin 11.
A cewar ƙungiyar, yayin da jami’o’in tarayya da wasu jami’o’in jihohi suka fara aiwatar da yarjejeniyar, har yanzu gwamnatocin wasu jihohin ba su biya alawus-alawus da sauran haƙƙoƙin malaman jami’o’i ba, waɗanda suka fara taruwa tun daga watan Janairun 2026.
ASUU ta bayyana cewa rassanta da ke jami’o’in da abin ya shafa sun fara shirye-shiryen shiga yajin aiki idan har ba a warware matsalolin ba cikin wa’adin da ta gindaya.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga gwamnonin jihohin da abin ya shafa da su gaggauta cika alƙawuran da suka ɗauka tare da biyan haƙƙoƙin malaman jami’o’i domin kauce wa tsaikon karatu da kuma kare tsarin ilimi daga shiga wani sabon rikici.
