News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane 150, Sun Kwace Babura 100 A Legas
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta sanar da kama mutane 150 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, tare da kwace babura 100 da ba a yi musu rijista a hukumance ba a wani samame da ta gudanar a sassa daban-daban na jihar.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abimbola Adebisi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an gudanar da samamen ne bayan tattara sahihan bayanan sirri kan ayyukan masu aikata laifuka.
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane 150, Sun Kwace Babura 100 A Legas
A cewarsa, manufar wannan aiki ita ce fatattakar masu laifi da suka addabi wasu yankuna na Jihar Legas tare da tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sanarwar ta bayyana cewa daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai babura 100 marasa rijista, wayoyin salula guda 54, bindigogi guda uku, kakin sojoji na bogi guda biyu, injinan janareta guda shida da ake kyautata zaton na sata ne, da kuma tabar wiwi tare da wasu nau’ikan miyagun ƙwayoyi masu gusar da hankali.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan dukkan waɗanda aka kama, kafin gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci hukunci bisa tanadin doka.
-
News7 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
Uncategorized3 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News5 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
