Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Cafke ‘Yar Afirka Ta Kudu Da Hodar Iblis Filin Jirgin Sama A  Abuja

Published

on

5af02544 c65b 4631 8635 e2d32ab47558 1783869981286

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama wata ‘yar ƙasar Afirka ta Kudu, Miss Will Jessica Ann, mai shekara 38, bisa zargin safarar hodar iblis mai nauyin kilogram 5.75 ta filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi cewa an kama wadda ake zargin ne a ranar Litinin, 6 ga Yuli, yayin binciken fasinjojin jirgin Qatar Airways da ya taso daga Doha zuwa Abuja.

Kudirin E-Health: Yadda Sanata Barau, “Sanatan Fasahar Zamani”, Ke Jagorantar Makomar Fasahar Kiwon Lafiya A Nijeriya

A cewar sanarwar, matar ta yi amfani da ɗanta mai shekara uku domin rage zargin jami’an tsaro yayin da take ƙoƙarin shigo da miyagun ƙwayoyin da aka ɓoye a cikin jakunkunanta.

NDLEA ta ce da farko matar ta musanta cewa jakunkunan nata ne. Sai dai bayan jami’ai sun tabbatar cewa alamun da ke jikin jakunkunan sun yi daidai da bayanan fasfo ɗinta, ta sauya maganarta tare da amincewa cewa ita ce mamallakinsu.

Ta kuma shaida wa jami’an bincike cewa ta taso ne daga ƙasar Cambodia, ta bi ta Doha kafin ta sauka a Abuja.

Advertisement

Bayanan sirri da hukumar ta tattara sun nuna cewa matar na cikin wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ta ƙasa da ƙasa tare da mijinta ko abokin zamanta, Jan Coenraad De Jager, wanda ke zaune a ƙasar Cambodia.

Rahoton ya ce ƙungiyar na amfani da hanyar Cambodia zuwa Afirka ta Kudu wajen safarar miyagun ƙwayoyi, yayin da binciken NDLEA ke ci gaba da nufin gano sauran mambobin ƙungiyar da kuma hanyoyin da suke bi wajen gudanar da haramtacciyar sana’arsu.

Hukumar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai wajen dakile fataucin miyagun ƙwayoyi tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a irin waɗannan laifuka domin fuskantar hukunci bisa tanadin doka.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending