News
Jami’an NDLEA Sun Cafke Muggan Kwayoyi Na Sama Da Naira Biliyan 10 Tashar Jiragen Ruwa Ta Apapa
Hukumar Hana Sha da Safarar Muggan Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta sanar da cafke wasu muggan kwayoyi da ake zargin nau’in Canadian Loud ne, waɗanda darajarsu ta kai kimanin naira biliyan 10.3, a wani samame da aka gudanar a tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas.
Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja. Ya ce jami’an NDLEA sun gano tare da ƙwace kwayoyin masu nauyin kilogiram 4,143.5, waɗanda aka ɓoye cikin ledoji 8,287 a cikin wani kwantena da aka shigo da shi daga ƙasar Kanada.
Ƴansanda Sun Kama Shugaban Hukumar PFIPC Ta Boge Adeniyi Bayan Umarnin Kotu
A cewarsa, an kama kayan ne a ranar 10 ga Yulin 2026, bayan wani aikin sa ido da bin diddigin kwantenan tun daga lokacin da ya taso daga birnin Montreal na ƙasar Kanada. Ya ce aikin ya samu nasara ne sakamakon haɗin gwiwar jami’an NDLEA, Hukumar Kwastam ta Najeriya da sauran hukumomin tsaro.
Babafemi ya ƙara da cewa jami’an NDLEA da ke aiki ƙarƙashin rundunar Directorate of Operations and General Investigation (DOGI) sun kuma dakile wani yunƙurin fitar da wasu muggan kwayoyi masu nauyin kilogiram 2.5 na nau’in Skunk, wani nau’in tabar wiwi (Cannabis), waɗanda aka ɓoye a cikin tukunyar iskar gas domin safararsu zuwa ƙasar Cyprus.
Ya bayyana cewa hukumar na ci gaba da gudanar da shirye-shiryen wayar da kan al’umma kan illolin shaye-shaye da safarar muggan kwayoyi a makarantu, masallatai, coci-coci, wuraren aiki da sauran al’ummomi a faɗin ƙasar.
A nasa ɓangaren, Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba da ƙoƙarin jami’an hukumar, musamman waɗanda ke aiki a Apapa da rundunar DOGI, tare da ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da tsaurara matakan hana shigowa da safarar muggan kwayoyi a Najeriya.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News2 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
