News
Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Biyu A Kan Babur
Mutane biyu sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a yammacin ranar Litinin a yankin Olorunsogo da ke unguwar Leme, a Karamar Hukumar Abeokuta ta Kudu, Jihar Ogun.
Rahotanni sun ce hatsarin ya afku da misalin karfe 5:45 na yamma, inda wata mota kirar Lexus ta yi karo da wani babur kirar TVS.
Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Biyu A Kan Bubar
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa motar Lexus na tafiya cikin tsananin gudu lokacin da ta bugi babur din. Direban babur ya mutu nan take bayan ya samu mummunan rauni a kansa.
Mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Ogun, Afolabi Odunsi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa mutane shida ne hatsarin ya ritsa da su, amma mutum biyu ne suka rasu, yayin da sauran suka tsira ba tare da samun raunuka ba.
Ya kara da cewa an kai gawarwakin mamatan zuwa dakin ajiye gawa na Asibitin Jiha da ke Ijaye, yayin da jami’an suka kwaso kayayyakin da aka samu a wurin, ciki har da katin shaida da wayar salula.
-
News5 days ago
Dakarun Soji Cafke Wani Shugaban ’Yan Ta’adda a Kaduna, Sun Kwato Harsasai 300
-
News6 days ago
Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu
-
News19 hours ago
Rundunar ‘Yansanda Ta Yi Gargaɗi Gam Da Yiwuwar Kai Hare-hare Makarantu Da Wuraren Ibada
