Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Ki Yadda Ya Gana Da Tawagar Shugaban Afirka Ta Kudu 

Published

on

Tinubu Bola 750x430

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙi ganawa da wata tawaga ta musamman da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya aiko zuwa Najeriya domin tattauna batun hare-haren kyamar baƙi da aka kai wa ‘yan Najeriya da sauran ‘yan Afirka a ƙasar.

Rahotanni sun bayyana cewa tawagar, ƙarƙashin jagorancin Ministan Harkokin Wajen Afirka ta Kudu, Ronald Lamola, ta isa Abuja ɗauke da saƙo daga Shugaba Ramaphosa.

Hukumomin Libya Sun Kori Baƙin-haure Fiye Da 117,000 Daga Ƙasar

Sai dai, maimakon ganawa da Shugaba Tinubu, an buƙaci tawagar ta miƙa saƙon ga Ƙaramin Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Sola Enikanolaiye.

Majiyoyi sun ce matakin ya biyo bayan rashin bin ƙa’idojin diflomasiyya, inda aka ce tawagar ta isa Najeriya ba tare da sanar da gwamnatin ƙasar a hukumance tun kafin zuwanta ba.

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa rashin sanarwa kafin isowar tawagar ne ya sa ba a shirya ganawa da Shugaba Tinubu ba.

Advertisement

Wannan ci gaba na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan rahotannin hare-haren kyamar baƙi da ake zargin ana kai wa ‘yan Najeriya da sauran ‘yan Afirka mazauna Afirka ta Kudu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending