News
Cutar Mashako Ta Hallaka Yara Sama Da 50 A Kano
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta daukar matakan dakile barkewar cutar mashako (Diphtheria) da ta hallaka sama da yara 50 a Karamar Hukumar Rano.
Majalisar ta yi wannan kiran ne a zaman da ta gudanar ranar Litinin, bayan dan majalisar da ke wakiltar mazabar Rano, Ibrahim Muhammad, ya gabatar da kudirin gaggawa kan barkewar cutar.
2027: Daraktocin RBDAs Sun Kafa Kungiya Don Tattara Kuri’un Manoma Miliyan 20 Ga Shugaba Tinubu
Dan majalisar ya ce lamarin ya yi tsanani musamman a al’ummomin Ridin da Sabuwar Kaura, inda ya ce sama da yara 50 suka rasa rayukansu sakamakon cutar.
Ya ce gwamnatin jihar ta riga ta dauki wasu matakan gaggawa, ciki har da sayen magunguna da tura ma’aikatan lafiya zuwa yankunan da cutar ta shafa.
Sai dai ya ce ana bukatar karin dauki daga gwamnati domin dakile ci gaba da yaduwar cutar da kuma kare rayukan al’ummar yankin.
Ya bukaci Gwamna Abba Yusuf da Kwamishinan Lafiya na jihar da su kara samar da tallafin gaggawa ga al’ummomin da cutar ta shafa.
Da yake goyon bayan kudirin, dan majalisar da ke wakiltar mazabar Kiru, Usman Abubakar Tasi’u, ya ce cutar ta fara yaduwa daga Rano zuwa Karamar Hukumar Kiru, ciki har da Kwarin Dangora, garin Dangora da Yelwa.
Ya bayyana cewa wani shugaban matasan jam’iyyar APC a garin Kiru ya rasa ’ya’yansa biyu sakamakon cutar cikin rana guda.
Tasi’u ya yi kira da a kafa wani kwamitin gaggawa domin daidaita kokarin dakile barkewar cutar a kananan hukumomin Rano, Tudun Wada, Kibiya, Bunkure, Bebeji da Kiru.
Daga karshe, Majalisar ta amince da kudirin tare da umartar Kwamitinta kan Lafiya da ya gana da Ma’aikatar Lafiya domin tabbatar da aiwatar da dokar da kuma samar da agajin gaggawa ga al’ummomin da cutar ta shafa.
-
Uncategorized6 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News5 days ago
Aƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
-
News1 day ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
