Connect with us

News

Rikicin Kan N200 Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 3 Da Ƙone-ƙone A Legas

Published

on

1788043386254

An kashe Mutane 3 wasu da dama sun jikkata bayan ɓarkewar rikici saboda Naira 200 a tsakanin ’yan daba (Area Boys) masu karɓar haramtaccen haraji a kan hanya da wani direban Adaidaita Sahu a yankin Ikola da ke Jihar Legas.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, (SP) Abimbola Adebisi, ya bayyana cewa rikicin ya faru ne a ranar Alhamis, biyo bayan wata taƙaddama mai zafi a tsakanin wasu Area Boys sun tilasta wa wani direban Adaidaita Sahu biyan haramtaccen harajin Naira 200.

2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC

SP Abimbola ya ce direban Adaidaita Sahu ɗin yi ƙi biyan Area Boys haramtaccen kuɗin, su kuma suka ƙwace abun hawansa.

Ya bayyana cewa direban Adaidaita Sahu ɗin ya yi tafiyarsa ya bar wa Area Boys ɗin abin hawansa da suka ƙwace, daga baya ya dawo tare da wasu mutane domin karɓar dukiyarsa.

A nan ne rikici ya barke tsakanin ɓangarorin biyu wanda ya haifar da mutuwar mutane uku tare da jikkata wasu da kuma cinna wuta ga wasu gine-gine na yankin.

Advertisement

Lamarin ya haifar da firgici da ya tilasta wa ɗaruruwan mazauna yankin tserewa domin neman mafaka.

Kakakin ’yan sandan ya ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Sojoji na Yaba domin ceton rayukansu a yayin da aka ajiye gawarwakin waɗanda suka rasu a ɗakin ajiye gawarwaki na Asibitin.

Ya ce tun ranar Alhamis da lamarin ya faru aka girke jami’an ’yan sandan jihar da haɗin guiwar sojoji da suka shawo kan lamarin.

Haka kuma Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legas, Tijani Olawole Fatai da Kwamandan Soja na Birget na 9, Birgediya Afolabi Owolabi sun ziyarci yankin na Ikola domin tantance irin ɓarnar da rikicin ya haifar.

Rundunar ’yan sandan ta yi kira ga jama’ar yankin su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da za su kai ga kama dukkan waɗanda ke da hannu wajen wannan rikici.

 

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending