Connect with us

News

FBI Ta Tabbatar An Taba Tuhumar Tinubu Kan Safarar Hodar Ibilis Da Halasta Kudaden Haramun

Published

on

fbi 750x430

Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta tabbatar da cewa an taɓa gudanar da binciken laifi kan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, dangane da zargin safarar miyagun ƙwayoyi a farkon shekarun 1990.

FBI ta bayyana hakan ne a wata rantsacciyar takarda da ta gabatar wa wata kotun tarayya a Amurka a ranar 28 ga Agusta, 2026, a wani shari’ar da ake yi ƙarƙashin dokar ’Yancin Samun Bayanai (FOIA), inda ake neman samun wasu takardun hukumar da suka shafi Tinubu.

Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice, Ya Taya Gwamnan Kano Da Al’umma Bikin Murnar Maulidi Annabi SAW

A cikin takardar, FBI ta ce bayanan da ake magana a kansu “an tattara su ne domin gudanar da binciken hukumar kan wasu mutane da dama dangane da laifukan safarar miyagun ƙwayoyi”.

Hukumar ta kuma ce kotun ta riga ta tabbatar da cewa an taɓa samun sahihin bayani a hukumance kan gudanar da bincike game da Bola Tinubu.

Matakin na baya-bayan nan ya biyo bayan hukuncin da Alƙaliyar Kotun Gundumar Amurka, Beryl Howell, ta yanke a watan Afrilun 2025, inda ta ce FBI da Hukumar Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi ta Amurka (DEA) ba za su ƙara amfani da tsarin da ake kira “Glomar response” wajen ƙin tabbatarwa ko musanta wanzuwar takardun binciken Tinubu ba.

Advertisement

Alƙaliyar ta ce hukumomin sun gaza gabatar da isassun dalilai na kare haƙƙin sirrin Tinubu da za su ba su damar ɓoye gaskiyar cewa an taɓa gudanar da binciken laifi a kansa.

Sai dai hukuncin kotun bai tabbatar da cewa Tinubu ya aikata laifin safarar miyagun ƙwayoyi ko kuma an taɓa yanke masa hukuncin wani laifi ba.

Binciken da ake magana a kai ya samo asali ne daga buƙatun bayanai da wani Ba’amurke mai fafutukar neman gaskiya, Aaron Greenspan, ya shigar ƙarƙashin dokar FOIA.

Daga cikin bayanan da Greenspan ke nema akwai “cikakken fayil ɗin FBI na Bola Ahmed Tinubu” da kuma bayanan tambayoyin da jami’an FBI suka yi da Tinubu tsakanin shekarun 1992 da 1993, ƙarƙashin shari’ar mai lamba 245-IP-71386-UUUUUU.

Buƙatun Greenspan na daga cikin wani yunƙuri mai faɗi na samun takardun bincike da suka shafi wata hanyar safarar hodar heroin da aka gudanar a Chicago a farkon shekarun 1990.

FBI ta ci gaba da hana fitar da wasu sassan takardun, tana mai dogaro da wasu tanade-tanaden dokar FOIA da suka shafi kare sirrin mutum, majiyoyin bayanan sirri, dabarun jami’an tsaro wajen gudanar da bincike da kuma bayanan da fallasa su ka iya jefa wasu mutane cikin haɗari.

Advertisement

Hukumar ta ce ba za ta iya bayyana cikakken dalilin da ya sa ta dogara da wasu daga cikin waɗannan tanade-tanaden ba.

Kamfanin da Atiku ya ɗauka ya wallafa takardar FBI

Kamfanin Von Batten-Montague-York, wani kamfanin hulɗa da gwamnati da ke Washington, wanda tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ɗauka gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027, ne ya wallafa wasu sassan takardar FBI.

Kamfanin ya bayyana a shafinsa na X cewa yana nazarin dimbin takardun da ya karɓa daga FBI, tare da cire wasu sassan da ake ganin ya kamata a kiyaye.

Kamfanin ya ce ya wallafa takardar ne domin ƙaryara iƙirarin cewa ba a taɓa gudanar da binciken laifi kan Tinubu ba.

Ya ce takardar ta nuna cewa FBI ta tabbatar a bisa rantsuwa cewa kotu ta riga ta tabbatar da cewa an taɓa amincewa a hukumance da gudanar da binciken laifi kan shugaban na Najeriya.

Advertisement

Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar da martani

Sai dai Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Sadarwa, Sunday Dare, ya yi watsi da iƙirarin da ake yaɗawa game da takardun FBI, yana mai cewa siyasa ce ta jawo batun.

Dare ya zargi Atiku da amfani da wani kamfanin hulɗa da gwamnati da ke Washington wajen ƙoƙarin haifar da ce-ce-ku-ce gabanin zaɓen 2027.

Ya bayyana yaɗa bayanan a matsayin wata kutungwilar siyasa, yana mai cewa takardun da ake yaɗawa ba su kasance wani sabon rahoton leƙen asiri ba.

Dare ya kuma yi tambaya kan sahihancin bayanan da kamfanin ke fitarwa, yana mai cewa bai kamata a ɗauki kalamansa a matsayin na gwamnatin Amurka ba.

Ya buƙaci masu yin zarge-zargen da su gabatar da hujjoji kan iƙirarin da suke yi, musamman waɗanda suka shafi bayanan leƙen asiri na sirri.

Advertisement

Dare ya kuma ce bayanan da ake samu a fili daga takardun Ma’aikatar Shari’a ta Amurka da suka shafi dokar rajistar wakilan ƙasashen waje (FARA) sun nuna cewa Atiku ya ɗauki kamfanin Von Batten-Montague-York kan kwangilar dala miliyan 1.2 na tsawon watanni 12.

A cewarsa, an ɗauki kamfanin ne domin ya taimaka wajen “daidaita” bayanan da gwamnatin Najeriya ke fitarwa tare da amfani da tsoffin bayanan kotunan Amurka wajen samun shiga a harkokin siyasa gabanin zaɓen 2027.

Dare ya kuma yi watsi da duk wata alaƙa tsakanin tafiyar Tinubu zuwa Turai da shari’ar FOIA, yana mai cewa shugaban yana hutun shekara-shekara ne da tun ba yanzu ba aka tsara.

Ya ce babu wata alaƙa tsakanin hutun shugaban a Turai da shari’ar da ake yi a kotun Amurka.

Dare ya kuma ambato lauyan Tinubu, Wole Afolabi, SAN, wanda ya yi bayani kan shari’ar a gidan talabijin na Channels, inda ya ce yunƙurin hana fitar da wasu sassan takardun yana da nasaba ne da dokokin Amurka da ke kare sirrin bayanan binciken jami’an tsaro.

A cewar Dare, Afolabi ya kuma ce da a ce Tinubu ya aikata wani laifi da ya sa ya zama abin hukunci a ƙarƙashin dokar Amurka, da hukumomin ƙasar sun gurfanar da shi a lokacin.

Advertisement

Dare ya zargi ’yan adawa da mayar da hankali kan tsoffin takardun Amurka maimakon gabatar wa ’yan Najeriya da cikakkun manufofin tattalin arziki da sauran shirye-shiryen da za su aiwatar idan suka samu mulki a 2027.

Ya ce ya kamata zaɓen ya ta’allaƙa ne kan yadda ’yan siyasa suka gudanar da mulki da kuma manufofinsu, ba wai ce-ce-ku-ce da ya shafi tsoffin bayanan binciken hukumomin ƙasar waje ba.

A halin yanzu, lauyoyin Tinubu na adawa da fitar da wasu ƙarin takardun, inda suka ce sakin wasu bayanan sirri da ke cikin taskar gwamnati zai keta haƙƙin shugaban na sirri.

 

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending