Connect with us

News

Sabon Rikici Ya Barke a APC a Gombe Kan Ware Sama da Kashi 95% na ’Yan Takarar Majalisa

Published

on

IMG 20261028 WA0007
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Wasu ’yan takarar kujerun Majalisar Dokokin Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar APC sun nuna rashin jin daɗi kan cire sama da kashi 95 cikin 100 na sunayensu daga cikin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen jam’iyyar, duk da ƙarin yawan mambobin kwamitin.

Ƙungiyar Forum of Concerned APC State Assembly Contestants, ƙarƙashin shirin One Gombe, One Mandate 2027, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken “Rejoinder: Exclusion of APC State Assembly Contestants from Campaign Council.”

Gwamnatin Tarayya Za Ta Riƙa Biyan Ma’aikata Tallafin Sufuri Naira 70,000 Duk Wata

Sanarwar ta nuna cewa an ƙara yawan mambobin kwamitin daga mutum 667 zuwa sama da 1,000, amma duk da haka an ci gaba da cire mafi yawan ’yan takarar Majalisar Dokokin Jihar.

Ƙungiyar ta yi tambaya kan dalilin da ya sa aka maimaita abin da ta kira kuskure a sabon jerin sunayen, tana mai cewa ya kamata a bayyana dalilin da ya sa matsalar ba ta samu gyara ba bayan sake fitar da jerin.

Ta zargi cewa ci gaba da cire ’yan takarar na iya zama wata hanya ta mayar da wasu ’yan jam’iyyar saniyar ware da rage musu tasiri a harkokin siyasa.

Advertisement

A cewar ƙungiyar, ’yan takarar Majalisar Dokokin Jihar na da muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa jam’iyyar a mazabu, haɗa kan jama’a da kuma gudanar da ayyukan yaƙin neman zaɓe a matakin rumfunan zaɓe.

Ta ce ’yan takarar sun yi aiki tukuru wajen tallafa wa jam’iyyar, ciki har da amfani da dukiyoyinsu wajen gudanar da ayyukan siyasa. Haka kuma, sun amince da sakamakon zaɓen fidda gwani ko tsarin yarjejeniya domin tabbatar da haɗin kan APC.

Sanarwar ta kuma nuna damuwa kan tasirin irin wannan mataki ga haɗin kan jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

“Ba za ku iya cin zaɓe ta hanyar ware sojojin ƙasa ba,” in ji ƙungiyar, tana mai jaddada cewa nasarar yaƙin neman zaɓe ta dogara ne da mutanen da ke aiki kai tsaye a mazabu da rumfunan zaɓe.

Duk da nuna rashin jin daɗin da suka yi, ƙungiyar ta ce mambobinta za su ci gaba da kasancewa cikin APC tare da biyayya ga jam’iyyar, amma ba za su yi shiru kan abin da suke ganin ba daidai ba ne ba.

Ta kuma bayyana cewa ba za ta bari lamarin ya haifar da rikici ba, tana mai cewa za ta ci gaba da neman goyon bayan jam’iyyar cikin lumana.

Advertisement

Ƙungiyar ta jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki domin ganin APC ta samu nasara a matakin ƙasa a zaɓen 2027.

“Mu ne APC. Muna nan a matsayin APC. Za mu yi aiki domin APC,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta fito ne daga Forum of Concerned APC State Assembly Contestants, One Gombe, One Mandate 2027, Jihar Gombe.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending