News
ICPC Ta Gurfanar Da Daraktan Hukumar ‘Bogi’ Kan Zargin Damfarar Naira Biliyan 30.8
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (ICPC) ta gurfanar da wani mutum mai suna Frins Matthew Adeniyi Adeyemi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin aikata laifuka 22 da suka shafi damfara, ƙirƙirar takardun bogi da kuma yin ƙarya kan kasancewarsa ma’aikacin gwamnati.
An gurfanar da Adeyemi ne a ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, 2026, a gaban Mai Shari’a Yusuf Halilu da ke zama a Maitama, Abuja.
Ƙungiyar Atiku Kano Business Forum Ta Karɓi Baƙuncin ’Ya’yan Atiku Abubakar A Kano
ICPC ta zarge shi da ƙirƙirar wata hukumar bogi mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), tare da yin amfani da takardun ƙarya wajen karɓar kuɗaɗen gwamnati da suka kai Naira biliyan 30.8.
A cikin tuhume-tuhumen da aka gabatar a kotun, hukumar ta ce wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa shi ne Darakta-Janar na PFIPC, inda ya yi amfani da wannan matsayi wajen neman kuɗaɗe da wasu abubuwan more rayuwa daga hukumomin gwamnati.
ICPC ta yi zargin cewa a ranar 8 ga Maris, 2024, a Abuja, Adeyemi ya ƙirƙiri wata wasiƙa mai lamba SH/COS/209/A/3456, wadda aka nuna cewa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne ya fitar ko ya sanya wa hannu.
A cewar hukumar, wasiƙar ta ƙunshi bayanan naɗa shi a matsayin Darakta-Janar na PFIPC, domin nuna cewa naɗin nasa sahihi ne, tare da ba shi damar amfani da kayayyakin ofishin gwamnati da ke Sakatariyar Tarayya, Phase II, Abuja.
Haka kuma, ICPC ta zarge shi da ƙirƙirar wasu takardu da ke nuna cewa PFIPC hukuma ce ta gwamnati mai cikakken izinin gudanar da ayyuka, ciki har da wata wasiƙa mai taken “Request for Approval of Self-Accounting Status” da aka aika wa Akanta Janar na Ƙasa.
Hukumar ta kuma yi zargin cewa Adeyemi ya ƙirƙiri takardun bogi da aka aika wa Darakta-Janar na Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA), domin samar da adireshin yanar gizo ga hukumar da ake zargin ba ta wanzu.
Baya ga haka, an zarge shi da bai wa wani jami’in Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF), mai suna Aminu Abdullahi, Naira 210,000 domin samun ofishi ga PFIPC ba tare da izinin hukumomin da abin ya shafa ba.
Haka kuma, ICPC ta zarge shi da bai wa wani jami’i a Ofishin Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tattalin Arziƙi, Ogaba Harry, Naira 300,000 domin samar masa da motocin alfarma guda biyu, wato Prado Jeep da Land Cruiser.
A wani ɓangare na tuhumar, hukumar ta ce a ranar 28 ga Yulin 2025, Adeyemi ya karɓi Naira miliyan 20 daga hannun Darakta-Manajan Kamfanin Divine Dopacy Nigeria Limited, Oyekunle Gbenga, bisa wani iƙirarin neman kuɗin gudanar da ayyuka.
ICPC ta ce kuɗin na da alaƙa da wata kwangila ta Naira biliyan 2.8 da PFIPC ta bayar domin sayen kayan ɗaki da na lantarki, da kuma gyaran wani gida da ake zargin an ba Adeyemi a matsayin gidan gwamnati.
Hukumar ta bayyana cewa zarge-zargen sun shafi abubuwan da ake zargin sun faru ne tsakanin shekarar 2024 da 2026, kuma sun saɓa wa tanade-tanaden dokokin Najeriya da suka shafi ƙirƙirar takardun bogi, damfara da cin hanci da rashawa.
Sai dai bayan an karanta masa tuhume-tuhumen guda 22 a gaban kotu, Adeyemi ya musanta aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su.
Bayan haka, lauyar masu ƙara, Fatima Bardi, ta roƙi kotun da ta sanya ranar fara shari’ar domin gabatar da hujjojin da ICPC ta dogara da su wajen tuhumar wanda ake zargin.
A nasa ɓangaren, lauyan Adeyemi, Ibrahim Angulu, ya nemi kotun da ta bayar da belinsa, yana mai cewa wanda yake karewa ya shafe kwanaki 155 a tsare kuma yana fuskantar ƙalubalen rashin lafiya.
Sai dai Mai Shari’a Halilu ya umarci lauyan da ya gabatar da buƙatar neman belin a rubuce domin kotu ta duba ta.
Daga bisani, alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 9 ga Nuwamba, 2026, domin fara shari’ar tare da duba buƙatar neman belin wanda ake zargin.

