News
An Kara Kudin Shiga Gidajen Kallon Kwallo A Kano
Ƙungiyar masu gidajen kallon wasannin ƙwallon ƙafa a Kano ta sanar da ƙarin kuɗin kallon ƙwallo daga Naira 200 zuwa Naira 500.
Wannan na cikin wata sanarwa da shugabancin ƙungiyar ya fitar, inda ya ce sabon tsarin zai fara aiki daga ranar Talata, 3 ga Nuwamba, sakamakon hauhawar kuɗaɗen gudanar da gidajen kallon.
Dakarun Soji Sun Hallaka Manyan Shugabannin Daesh A Borno
Ƙungiyar ta ce ƙarin kuɗaɗen da ake kashewa wajen biyan kuɗin tashoshi, lasisi, haraji da wutar lantarki ne suka sa aka ɗauki matakin ƙara kuɗin shiga.
Sai dai binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa wasu gidajen kallon ƙwallo a unguwanni daban-daban na cikin birnin Kano sun ƙara kuɗin shiga da Naira 100 kacal, inda ya tashi daga Naira 100 zuwa Naira 200.
A Ƙaramar Hukumar Bichi kuwa, shugaban ƙungiyar masu gidajen kallon ƙwallo, Murtala Maijangwam Bichi, ya ce kuɗin shiga zai tashi daga Naira 100 zuwa Naira 200.
Ya kuma roƙi al’ummar yankin da su fahimci sabon tsarin, la’akari da ƙarin kuɗaɗen da ake kashewa wajen gudanar da gidajen kallon.

