Sports
Gwamnatin Kano zata siyawa Katsina United sabuwar mota
Daga Khadija abdullahi muhmd
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yayi Allah wadai da lalata motar kungiyar kwallon kafa ta Katsina United a yayin da kungiyar kwallon kafa ta Kano pillars ta karbi bakuncinta a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.
Gwamna Ganduje yace zasu kafa kwamiti mai karfi don binciko musabbabin hatsaniyar da ta faru a wasan da Kano Pillars tayi da Katsina United a makon da ya gabata.
A cikin wata sanarwa da sakataran yada labaran gwamna Abba Anwar ya fitar ya ce gwamnatin Kano zata siyawa Katsina United sabuwar mota.
Advertisements
