Connect with us

News

Sagagi zai cigaba da kasancewa shugaban PDP a Kano har karshen 2024 — Kotu

Published

on

 

Daga Hamza Yusuf Abdulmumin

 

 

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja, ta jaddada batunta na hana uwar jam’iyyar PDP ta kasa cire shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Shehu Wada Sagagi, daga mukaminsa, har sai ya kare wa’adinsa kamar yadda doka ta tanadar, inda zai sauka a watan Disambar shekarar 2024, kasancewar an zabe shi ne tare da sauran kunshin shugabancinsa a ranar 14 ga watan Disambar shekarar 2020.

Da yake yanke hukunci a yau Laraba, mai shari’a Jostis Taiwo Taiwo, yace kwamitin kolin jam’iyyar PDP ko wani sashi na jam’iyyar, bashi da ikon sauke duk shugaban da aka zaba ta hanyar da aka amince, saboda haka Sagagi da sauran shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Kano sune shugabanni har zuwa karewar wa’adinsu.

Advertisement

Sagagi dai na fuskantar shari’a a wannan tsakanin, kasancewar wani tsagin jam’iyyar a jihar Kano na zarginsa da yin aiki da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya koma jam’iyyar NNPP, abinda Sagagin ya musanta.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending