Connect with us

News

Mohammed Salah: Ina nan daram a Liverpool

Published

on

Daga Usman Abdullahi jibirin

 

 

 

Dan kwallon Liverpool, Mohammed Salah ya ce “tabbas” zai ci gaba da kasancewa a kungiyar a kakar wasa mai zuwa amma kuma ya ki bayyana ko zai sabunta yarjejeniyarsa ko kuma a’a.

Yau za a gudanar da zaben fitar da gwani na gwamnoni a APC

Advertisement

Yarjejeniyar Salah da Liverpool za ta kare ne a watan Yunin 2023 abin da ya janyo ake jita-jitar zai bar Anfield.

“Tabbas zan kasance a nan a kakar wasa mai zuwa. Abin da ke gabanmu shi ne lashe gasar Champions”.

Takwaransa dan kasar Senegel, Sadio Mane, ya ce zai bayyana matsayinsa kan ganiyar bayan sun taka leda da Real Madrid a birnin Paris.

Mohamed Salah ya zura kwallo 31 a Liverpool a kakar bana sannan Sadio Mane ya zura 23

Dan kwallon Senegal din ya zura kwallo 120 a cikin wasa 268 da ya buga wa Liverpool kuma kungilarsa da kungiyar za ta kare ne a watan Yunin badi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending