News
Sha’aban Sharada ya kai ziyarar bazata wajen zaɓen fidda-gwani na gwamna a Kano
Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyar APC, kuma ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Kano Municipal, Sha’aban Sharada, ya kai ziyarar bazata wajen da za a gudanar da zaɓen fidda-gwani na gwamna a jihar.
2023: PDP Ta Tsayar Da ’Yan Takarar Gwamna 2 A Kano
Jaridar Indaranka ta rawaito cewa za a gudanar da zaɓen ne tsakanin Mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, kuma ɗan takarar gwamna a APC a jihar da kuma Sharada.
Zaɓen dai zai gudana ne a filin wasa na indoor Stadium da ke Kofar Mata a birnin Kano a yau Alhamis.
Sai dai kuma wasu hotuna da su ka fara yawo a kafafen sadarwa sun nuna Sharada, tare da muƙarrabansa, ya shiga wajen da za a gudanar da zaɓen, domin duba irin shirin da a ka yi a zaɓen.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne dai ya tsayar da Gawuna, da tsohon Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Murtala Sule Garo a matsayin waɗanda za su yinwa APC takara a APC.
Sannan shima Sharada, wanda ya ke cikin ɓangaren G-7 a APC, ya tsaya takarar, inda a yau ne za a raba raini tsakaninsu domin fitar da wanda zai jagoranci jam’iyar a zaɓen gwamna na 2023 a jihar.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
