Connect with us

News

Tsohon hadimin Buhari ya sha kaye a zaben fidda gwani na APC

Published

on

Daga yasir sani Abdullah 

 

Tsohon hadimin shugaban Najeriya kan kafafen sada zumunta Bashir Ahmed da ke nemna takarar dan majalisar wakilai ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwani da aka yi a inda zai wakilta.

Sabbin sauye-sauyen da Saudiyya ta shimfida wa mahajjatan bana

Bashir Ahmed wanda ke neman wakiltar kananan hukumomin Gaya da Ajingi da Albasu ne a matsayin tarayya, ya kafa hujjar rikici a matsayin dalilin da ya sanya ya yi watsi da sakamakon.

Rahotanni sun bayyana cewa an kasa cimma maslaha tsakanin ‘yan takara da dama a mazabu masu yawa.

Ciki kuwa har da Fagge da Kano Municipal da Baya da Ajingi da Albasu, Kiru da Bebeji da dai sauransu.

Advertisement

Ya yi zargin kawo ‘yan daba domin tayar da hankali da ganin ba a yi zaben ba yadda ya kamata, ya ce hakan yasa ya fice daga dakin zaben saboda tsaro.

An bayyana dan majalisar tarayya da ke ci a yanzu Abdullahi Mahmood Gaya a matsayin wanda ya lashe zaben.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending