Sports
Carlos Tevez ya sanar da yin ritaya daga taka leda
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Tsohon dan wasan tawagar Argentina da Manchester United da Manchester City da West Ham, Carlos Tevez ya sanar da yin ritaya daga taka leda.
Rabon da Tevez mai shekara 38 ya taka leda tun bayan Yunin 2021, bayan da ya bar kungiyarsa da ya fara wasa tun yana matashi Boca Juniors.
Dan kwallon ya sanar cewar ya yi dukkan abin da zai yi a kwallon kafa, amma mutuwar mahaifinsa a bara, tana daga dalilin da ya ajiye takalma, duk da wasu kungiyoyi sun bukace shi.
Tevez ya taka leda a Juventus da kungiyar Brazil, Corinthians da zuwa Boca Juniors karo biyu da Shanghai Shenhua ta China.
A shekarar 2004, Tevez ya lashe lambar zinare a Olympic a Athens tare da Argentina, wadda ya yi wa wasa 75.
Advertisements
