Connect with us

News

Rikici Ya Barke Tsakanin Shugaban APC Na Jihar Kano Da Jami’an Tsaro A Taron APC

Published

on

Daga mujahid danlami garba 

 

 

 

 

An dakatar da jefa kuri’a a zaben fid-da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC bayan barkewar wata takaddama tsakanin shugaban jam’iyyar na Jihar Kano, Abdullahi Abbas da jami’an tsaro a zauren taron.

Advertisement

Hatsaniyar ta tashi ne kan zargin magudi a yayin da daliget suke jefa kuri’a a zauren taron da ke gudana a Abuja.

Ƙarancin dakon man fetur ne ya haifar da wahalarsa a ƙasa  — IPMAN

Daga baya kwamitin gudanar da zaben fitar da dan takarar ya shawo kan rikcin.

Sai dai kuma ya umarci duk wasu jami’an jam’iyyar da ke sanye da shudin riga su bar wurin da aka ware domin jefa kuri’a.

Daga bisani aka ci gaba da jefa kuri’a da aka fara da daliget din Jihar Legas tun da misalin karfe 2 na dare.

Jihar Kano na da daliget 127 da suka jefa kuri’a a zaben da ke gudana a safiyar ranar Laraba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending