News
Kwale-kwale ya nutse da mai ciki da wasu mutum biyar a Bayelsa
Daga Yasir sani abdullahi
Rahotanni daga yankin karamar hukumar Ijaw ta Kudu a jihar Bayelsa da ke Kudancin Najeriya na cewa mutum shida da suka hada da wata mace mai ciki sun nutse a ruwa, bayan da kwale-kwalensu ya kife.
Advertisements
Advertisements
Hatsarin ya faru ne ranar Asabar da rana.
Jaridun cikin gida sun ruwaito cewa yanzu haka masu aikin ceto na kan neman matafiyan, da suka hada da wata mai hidimar kasa da kuma dattijuwa mai shekara 70.
Advertisements
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda a jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa suna jiran karin bayani kan bayanan mutanen da lamarin ya rutsa da su.
Advertisements
Advertisements
Advertisements
