News
Tinubu: Na koma ga Allah lokacin da na ga wasu na neman hana ni takarar shugaban Najeriya
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Dan takarar shugaban kasa a Najeriya karkashin jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ce ya koma ga Allah a lokacin da ya lura cewa wasu sun hada kai suna son ganin bai tsaya takarar shugaban kasa na jam’iyyar ba.
Tinubu ya ce ya fahimci cewa an shirya yi masa taron-dangi don ganin bayansa kan takarar shugaban kasa da yake son yi.
Gboyega Akosile, sakataren yada labarai na gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu ya ambato Tinubu na yin wadannan kalaman a lokacin da ya kai wa Oba na Lagos Rilwan Akiolu ziyara, kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
Tsohon gwamnan na Jihar Lagos ya doke mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; tsohon Ministan ma’aikatar Sufuri, Rotimi Amaechi; shugaban majaliasar dattawa Ahmad Lawan da wasu ‘yan takara 10 a zaben fitar da gwani.
“Babu wani dan asalin Jihar Lagos da ya samu damar zama shugaban Najeriya, duk da irin gudunmawar da jihar ta bayar wajen ci gaban kasar,” a cewar Mr Tinubu.
“Mukami mafi girma da wani dan Jihar Lagos ya rike a Najeriya shi ne na Alkalin Alkalan Tarayya. Na sha alwashin karya wannan alkadari.
“Fafutukar da muka yi ta neman tikitin takara a APC tana da matukar wahala. Lokacin da na kusa karaya, Na mayar da hankali ga addu’o’i. Kazalika na fadi abin da ke zuciyata lokacin da na ji cewa ana yi mini taron-dangi.”
Tinubu ya kara da cewa abu mafi muhimmanci yanzu shi ne ‘yan Najeriya su zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
