Connect with us

News

Shugaba Buhari zai tafi Rwanda

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai halarci taron shugabannin ƙungiyar Commonwealth ta ƙasashe rainon Ingila da ke gudana a ƙasar Rwanda daga 20 zuwa 26 ga watan Yuni.

Advertisement

.Jam’iyyar NNPP Tayi Allah-Wadai Da Korar Malaman Makaranta Sama Da Dubu Biyu A Jihar Kaduna

Wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar a yau Laraba ta ce shugaban zai halarci buɗe bikin a hukumance ranar Juma’a.

 

Taron mai laƙabin CHOGM 2022, zai tattauna kan halin rayuwa da kuma ci gaban al’ummar ƙungiyar fiye da biliyan biyu da ke zaune a ƙasa 54 na nahiyoyin Afirka da Asiya da Amurka da Turai da kuma yankin Pacific.

 

Ministci da manyan jami’an gwamnatin Najeriya takwas ne za su yi wa Buhari rakiya zuwa Rwanda.

Advertisement

 

Ana sa ran shugaban zai koma Najeriya ranar Lahadi, 26 ga watan Yuni.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending