News
Na tsallake rijiya da baya a wajen yaran gawuna
Daga Yasir sani Abdullahi
Tsohon mataimakin Ganduje yasha dakyar a hannun tawagar Gawuna
Jaridar daily trust Hausa ta rawaito cewa Tsohon mataimaki na musamman ga gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a bangaren kula da Makabartu, S.A Alhajiji Nagoda, ya zargi mutanen dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar APC, kuma mataimakin gwamna, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, da kai masa farmaki a wannan rana.
Alhajiji yace lamarin ya faru ne a wajen zaman ta’aziyyar rasuwar kanwar Mahaifiyarsa, wanda Gawuna yazo ta dalilin guda cikin ‘ya’yan mai rasuwar, inda yaransa suka farmake shi, amma yace ya tsallake rijiya da baya.
Alhaji nagoda ya kasance Daya ne daga cikin masu raje kare tsohon gwamnan kano Dr rabiu Musa kwankwaso
Kuma ya kasan ce tsohon Mai bada shawarwari ga makabartu
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
