Connect with us

News

An kawo ƙarshen yunƙurin haɗewa tsakanin Kwankwaso da Obi’

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Labour Doyin Okupe, ya ce an kawo ƙarshen yunƙurin da ake yi na haɗewa tsakanin jam’iyyar Kwankwaso ta NNPP da ta Peter Obi wato LP.

Advertisements
Advertisements

Yayin wani shirin siyasa na kafar talabijin din Channels jiya Talata Mista Okupe ya ce tun kusan makwanni hudu da suka gabata aka kawo ƙarshen yunƙurin, amma sai ƴan jam’iyyar NNPP suka ci gaba da yaɗa arfaganda a kan batun dn ganin sun raɓa kansu da farin jinin da Mista Obi ke da shi a wajen yan Najeriya.

Ya ce Kwankwaso ya ki amincewa ya zama mataimakin shugaban ƙasa ga Obi ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili da ya wuce saboda shi dan arewa ne ba.

”Ni na jagoranci ɓangarenmu na LP a wannan tattaunawa, daga lokacin da na nuna musu cewa yanzu lokaci ne da ya kamata a mika mulki ga yankin kudancin Najeriya amma suka ƙi amincewa muka nuna sasantawar ba za ta yiwu ba” in ji Mista Okupe.

Advertisements
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending