Yau ne shugaban Najeriya Muhamadu Buhari zai kama hanyar zuwa Senegal, don halartar taron ƙungiyar samar da ci gaban ƙasa da ƙasa ta IDA
Shugaban zai bar Najeriya ne a dai-dai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-hare a ƙasar, inda a ƙasa da awanni 24 aka kai hari gidan yarin Kuje da ke babban birnin kasar Abuja, aka kai wa tawagarsa hari a jihar Katsina, sannan kuma aka halaka mataimakin kwamishinan yan sanda na jihar
